Jose Peseiro ya ce babban alfahari ne da ya horar da Super Eagles bayan ya tabbatar da barin aikin tawagar kwallon kafar Najeriya.
Pulse Sports Nigeria ta ruwaito cewa Najeriya za ta nemi sabon koci bayan ta kasa sabunta kwantiragin Peseiro a matsayin kocin Super Eagles.
Kocin dan kasar Portugal din ya sanar da kawo karshen mulkin sa na tsawon watanni 22 ta shafin Facebook da yammacin ranar Juma’a.
Peseiro ya jagoranci Najeriya zuwa wasan karshe na gasar cin kofin Afrika da aka buga a baya-bayan nan, inda ya maido da imani bayan rashin nasarar da kungiyar ta yi a gasar da ta gabata.
Kuma duk da kiraye-kirayen da ake yi masa na ya ci gaba, mai shekaru 63 ya bayyana cewa tafiyarsa ta Najeriya ta zo karshe.