Jam’iyyar PDP ta zaba dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, abokin takararsa da za su fafata a zaben 2023.
Wadanda ke kusa da kamfen dinsa sun ce za a sanar da hakan ne da tsakar rana, sannan kuma kwamitin da aka riga aka kafa domin tantance shi zai tantance wanda ya zaba.
Hakan ya biyo bayan kammala daren Larabar da ta gabata ne aka yi jerin gwano tsakanin dan takarar da shugabannin jam’iyyar kan lamarin.
PREMIUM TIMES ta rawaito cewa, gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a safiyar yau Alhamis ne za a gabatar da shi.
“Mista Okowa ne zai zama wanda za a gabatar da shi a safiyar yau,” in ji wani amintaccen mai gudanar da yakin neman zaben wanda ya san lamarin ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Paul Ibe, mai magana da yawun ofishin yada labarai na Atiku, ya ki cewa uffan game da wanene dan takarar mataimakin shugaban kasa, yana mai cewa PREMIUM TIMES ta jira sanarwar a hukumance.