Tsagin Ambasada Aminu Wali, a jam’iyyar PDP, sun bukaci uwar jam’iyyar ta kasa, da ta rushe shugabancin ta na jihar Kano.
Kadaura24 ta rawaito da ya ganawa da manema labarai a Abuja, Alhaji Yahaya Bagobiri yace sun gabatar da koken ne Saboda da yadda aka baiwa yan Kwankwasiyya Umarnin komawa jam’iyyar NNPP Kuma har sun Fara yankar katin jam’iyyar.
Bashir Sanata, shi ne kakakin jam’iyyar a nan Kano yace tsagin Aminu Wali basu zabi PDP a zaben gwamna na shekarar 2019 ba, sun marawa gwamna Ganduje baya ne a jam’iyyar APC Idan batu ake na barin jam’iyyar PDP.
Waɗannan korafe-korafe ne yasa uwar jam’iyyar ta kasa ta kirowa kowanne bangare helkwatar jam’iyyar dake wadata plaza a Abuja domin Jin bahasi .
Uwar jam’iyyar ta karbi korafe-korafen kowanne bangare, ta kuma ce zata yiwa kowanne bangare adalci wajen zartar da hukuncin da ya kamata.
Shehu Wada Sagagi dai shi ne Shugaban jam’iyyar ta PDP Kuma yana biyayya ne ga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.