Jam’iyyar PDP ta naɗa Sanata Shu’aibu Lau, na Taraba ta Arewa a matsayin sabon mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa ta kasa.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa, kujerar ta zama babu kowa biyo bayan sauya shekar mai rike da ita a baya, Sanata Emmanuel Bwacha na Taraba ta Kudu zuwa APC a ƙarshen mako.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawal, shi ne ya karanta wasikar naɗin daga shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu.
Lawan ya bayyana Sanata Bwacha a matsayin sabon mamban jam’iyyar APC a hukumance a zaman majalisar na yau Talata. Shugaban majaisa ya umarci Sanata Orji Kalu ya kai Bwacha sabuwar kujerarsa a sashin da aka ware wa mambobin jam’iyya mai mulki.