fidelitybank

Da Dumi-Dumi: PDP ta mika sunayen mutane 2 da za su maye gurbin gwamnan Ebonyi

Date:

Jam’iyyar PDP ta mika sunayen mutane biyu da ta tantance, domin maye gurbin gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi da mataimakinsa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

A safiyar ranar Talata ne mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar da umarnin tsige Umahi daga mukaminsa sakamakon sauya sheka da ya yi zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a watan Nuwamba 2020.

Ya ci gaba da cewa, kundin tsarin mulkin kasar bai amince da mika katin zabe daga wata jam’iyya zuwa wata ba.

Alkalin ya kuma umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta karbi sunayen mutane biyu daga jam’iyyar PDP da za su maye gurbin Umahi da Eric Igwe a matsayin gwamna da mataimakin gwamna.

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wani taron manema labarai a Abuja, ya ce jam’iyyar ta zabi Iduma Igariwe da Fred Udogwu a matsayin gwamnan Ebonyi kuma mataimakin gwamna ga INEC.

Ayu ya ce: “Bayan shawarwarin da shugabannin jam’iyyar na kasa suka yi da sauran masu ruwa da tsaki, mun yanke shawarar gabatar da Hon. Iduma Igariwe da Fred Udogwu na mukaman gwamna da mataimakin gwamna a jihar Ebonyi.”

fg spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp