Jam’iyyar PDP ta dage taron da ta shiryagudanarwa a shiryyar Arewa maso Yamma a ranar Asabar.
Punch ta rawaito cewa, kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa a ranar Juma’a ya dage taron gangamin na shiyyar Arewa maso Yamma, wanda a ka shirya yi a ranar Asabar, 12 ga Fabrairu, 2022.
Hakan na zuwa ne a wata sanarwa da Sakataren jam’iyyar na kasa Umar Bature ya sanyawa hannu a ranar Juma’a mai taken ‘Postponement of Northwest zone Congress’.
Duk da cewa jam’iyyar ba ta bayyana dalilan dage taron ba, amma a na iya alakanta dagewar da zaben 2022 na majalisar tarayya da za a yi a rana guda.