Olisa Metuh, tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa ya fice daga jam’iyyar.
Metuh ya bayyana cewa zai kara ba da gudunmawa ga harkokin mulkin Najeriya ta hanyar rashin bangaranci.
A wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, Metuh ya koka da yadda siyasar Najeriya ke tabarbarewa.
Ya yi nuni da cewa ba zai iya kara shiga harkokin siyasar bangaranci ba.
A cewar Metuh: “A ziyarar da na yi na tsawon makonni uku saboda dalilai na lafiya da na kashin kai, na fahimci cewa ba zan iya kara yin siyasa ba a Najeriya.
“Dalilin da ya sa na yanke wannan shawara shi ne, daga gogewa na da kuma yanayin siyasa da ci gaban Najeriya, na yi imanin cewa zan kara ba da gudummawa ga dimokuradiyya da shugabanci na gari a Najeriya ta hanyar rashin bangaranci.
“A kan haka, na rubuta cikin girmamawa domin in sanar da ku ficewara daga jam’iyyar PDP da kuma daina siyasar bangaranci.
“Kamar yadda kundin tsarin mulkin PDP ya tanada, na mika kwafin murabus na ga shugaban gunduma ta.”
A shekarar 2016, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, ta gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin almundahanar Naira miliyan 400.
EFCC dai ta zargi Metuh da karbar makudan kudade daga ofishin tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA.
Sai dai Metuh ya musanta karbar kudaden, yana mai jaddada cewa tsohon ofishinsa ne ya tattara kudaden ya kuma yi amfani da su wajen gurfanar da shi gaban kotu.
Duk da musanta zargin, an yanke wa tsohon kakakin PDP hukuncin zaman gidan yari a shekarar 2021 bayan an same shi da laifuka bakwai na karkatar da kudade.