Sabuwar jam’iyyar adawa ta NNPP na gudanar da babban taronta na kasa a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya.
Ana gudanar da taron ne a filin wasa na Moshood Abiola da ke birnin Abuja.
A wannan taron ake sa ran daliget za su zabi mutumin da zai tsayawa jam’iyyar takarar shugaban kasa, duk da cewa ana ganin tabbatarwa kadai za a yi sakamakon Sanata Kwankwaso ne kadai É—an takararta.
Ana sa ran daliget 774 ne za su hallara a wurin taron daga duka kananan hukumomin Najeriya.