Hukumar shirya jarabawar kammala sakandiri ta kasa NECO, ta ce, dage jarabawar da aka yi niyar gudanar wa a ranar Asabar, 9 ga watan Yuni, 2022 wadda ta ayyana ranar Sallah (Eid-Adha).
Hukumar ta ce, an yi hakan ne domin bai wa Musulmi damar samun isasshen lokaci don gudanar da bukukuwan sallah.
Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NECO, Azeez Sani ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO), ta bayyana cewa, ba ta sanya ranar da za a yi jarrabawar ba, a ranar Asabar 9 ga watan Yuli, 2022.
“Wannan ya sabawa rade-radin da ake yi a wasu bangarori na cewa, Majalisar ta tsara jarabawar ranar 9 ga Yuli, 2022, wato ranar Sallah (Eid-Adha).