Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, ta damke katan 22 na Hodar Iblis na heroin, da kudin ta ya haura Naira biliyan 4.5 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Ikeja, Legas.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Hukumar NDLEA, Mista Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Babafemi ya ce, kayan da aka boye a cikin fakitin abincin jarirai na Nestle Cerelac, nauyinsu ya kai kilogiram 23.55.
Ya c,e kayan sun fito ne daga birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a cikin jirgin na South African Airways ranar Laraba 29 ga watan Yuni.
Wannan, a cewarsa, wani bangare ne na hadakar kayayyakin da suka isa rumfar shigo da kaya ta Skyway Aviation Handling Company Plc na filin jirgin saman Legas.
“Bayan bin diddigin ayyukan da suka kai ga kama wasu ma’aikatan sufurin kaya biyu, ainihin wanda ya karbi maganin shine Chike Eweni.
“Eweni, wanda ke rarraba wa abokin aikin sa na Afirka ta Kudu, an kama shi ne washegarin ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, a wani kantin sayar da kayayyaki da ke Ajao Estate, Ikeja.