fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Mutane hudu sun mutu 12 sun jikkata a fashewar Tankar Mai

Date:

Ana fargabar mutane hudu sun mutu, yayin da wasu 12 suka samu raunuka daban-daban, sakamakon fashewar wani abu a kasuwar sinadarai ta Onitsha a ranar Talata.

Majiyoyi sun shaidawa DAILY POST cewa, fashewar ta yi sanadin tashin gobara a yankin, tare da lalata kayayyaki sama da Naira miliyan 850 a cikin aikin.

Fashewar ta afku ne da misalin karfe 12:45 na rana a kasuwar, lamarin da ya kai ga turmutsutsu, daga bisani kuma ta yi aman wuta, kamar yadda wata majiya ta bayyana.

Ya kara da cewa mutane hudun sun mutu ne sakamakon turmutsitsin da ‘yan kasuwa suka yi domin tsira da rayukansu.

“Shugaban karamar hukumar Onitsha ta Kudu, Mista Emeka Orji ya tuntubi shugaban hukumar kashe gobara na jihar Anambra, Martin Agbili, wanda ya tura jami’an sashen daga Okpoko a karamar hukumar Ogbaru da kuma na Asaba a jihar Delta.

“Shugaban majalisar ya kuma tuntubi Baturen ‘yan sanda Fegge, Rabi’u Garuba wanda ya tura jami’ai da mazaje kasuwar domin tabbatar da tsaron kayayyaki da sauran kadarorin ‘yan kasuwar,” inji majiyar.

Wani dan kasuwa wanda ya zanta da wannan dan jarida, Mista Nweke Uchenna ya ce: “Muna cikin shagunanmu kamar yadda muka saba sai muka ji wata kara kamar tashin bam sai muka ga hayaki mai kauri daga wasu shaguna a sama, kowa ya fara gudu don tsira.

“Daga nan sai mutane suka fara ihun neman agaji, sai muka ga mutane dauke da ‘yan kasuwa daga cikin shagunan da suka kone, wasu kuma sun kone kurmus, yayin da wasu da alamun hayaki da turmutsutsun suka shake su.

“Ba mu san nawa ne gobarar ta yi hasarar ba amma ana iya kiyasin Naira miliyan 850 zuwa kusan Naira biliyan 1 saboda kayayyakin suna da karfi da sinadarai da ke da zafi sosai,” inji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, DSP Toochukwu Ikenga ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce: “Ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba a yanzu, amma jami’an mu karkashin jagorancin DCP John Ogbodoaga suna nan, kuma an shawo kan lamarin.”

sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...
X whatsapp