An tabbatar da mutuwar mutane bakwai ciki har da mace daya tare da jikkata wasu da dama, bayan wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai hari kauyen Tor Damisa, dake karamar hukumar Donga a jihar Taraba.
Wannan harin ramuwar gayya da makiyayan suka kai kan al’ummar Tiv, na zuwa ne kwanaki bayan da wasu da ake zargin ‘yan kabilar Tibi ne suka ji wa wani makiyayi rauni a lokacin da yake kiwon shanunsa a kan kuryar kauyen.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abdullahi Usman wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels ta wayar tarho a ranar Talata ya kuma bayyana cewa an kona gidaje.
A cewarsa, a halin yanzu ‘yan sanda da sojoji da kwararrun mafarauta suna bin maharan da nufin kama su tare da gurfanar da su gaban kuliya.