Mutum biyu ne suka mutu, sakamakon ruftawar da kasa ta yi a kansu, a karanar hukumar Bichi da ke jihar Kano.
rahotonni sun ce mutanen suna cikin wani rami ne inda suke tonon dutse lokacin da kasar da rufta kansu.
Jami’an ‘yan sanda sun dauki gawarwakin zuwa babban asibitin Bichi. In ji BBC.
A watan Maris din da ya gabata, an samu makamancin wannan lamari inda abokai hudu suka mutu lokacin da suke tonon kasar da za su yi wa abokinsu da zai yi aure daki.