Rikicin da ya barke tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a yankin Zak da ke karamar hukumar Wase ta Jihar Filato ya yi sanadiyar mutuwar mutane goma sha biyu.
A cewar wata majiya, lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar Lahadi, inda ya kai ga kashe ‘yan bindiga tara da ‘yan banga uku, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Mai magana da yawun rundunar ‘Operation Safe Haven’ (OPSH), Manjo Ishaku Takwa, jami’an tsaro da dama da ke wanzar da zaman lafiya a jihar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ba zai iya bayyana adadin wadanda abin ya shafa ba.
Ya bayyana cewa sojojin sun dakile harin.
Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun bayar da sanarwar barin kauyukan Sabon Zama, Gindin Dutse, Anguwar Tsohon Soja, Anguwar Yuhana da Anguwan Mangu na Wase da su fice daga yankunansu ko kuma su fuskanci yaki.