Kungiyar NUPENG ta zargi ma’aikatar ayyuka da gidaje da kokarin sace Naira biliyan 621 na gyara hanyoyin kasar nan.
Shugabannin NUPENG sun fitar da jawabi, suka ce muddin aka taba wannan kudi, za a shiga yajin-aiki.
A na zargin jami’an gwamnati da karkatar da wadannan kudi, wajen kwangilolin da su ke zargi sun cinye kudinsu.
A ranar Lahadi, 13 ga watan Fubrairu 2022, kungiyar NUPENG ta ma’aikatan man fetur da Gas a Najeriya ta nuna goyon bayanta a kan tafiya yajin aiki.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, kungiyar NUPENG ta na goyon bayan direbobin tankokin mai su tafi yajin-aiki, domin nunawa gwamnati rashin jin dadinsu.