Lionel Messi zai koma Barcelona a bazara mai zuwa, bayan ya yi ganawar ‘zaman lafiya’ da shugaban kungiyar, Joan Laporta.
Messi ya bar Nou Camp a matsayin wakili na kyauta a bara don kulla yarjejeniya da Paris Saint-Germain.
A lokacin, Barca ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa dan wasan mai shekaru 35 zai tafi ne saboda takunkumin kudi da LaLiga ya sanya musu.
Sai dai yanzu Messi na shirin komawa kungiyar ta La Liga idan kwantiraginsa da PSG ya kare a bazara mai zuwa.
A cewar wata ‘yar jarida dan kasar Argentina, Veronica Brunati, dan wasan zai koma Barcelona a ranar 1 ga Yuli, 2023, bayan shekaru biyu kacal a Paris Saint-Germain.
An yi imanin Messi zai koma kulob din bayan ya yi sulhu da Laporta, wanda ke tsakiyar rikicin shekaru biyu da suka wuce.