Wasu mata da jami’an tsaro su ka tsare mazajensu fiye da shekara ɗaya ba tare da shari’a ba, na gudanar da zanga-zanga a Jihar Kano.
Wasu daga cikin matan sun fito ne tare da ‘ya’yansu ƙanana maza da mata.
A 2021 ne wata kotu a Dubai da ke ƙasar Daular Larabawa (UAE) ta yanke wa wasu ‘yan Najeriya hukunci, ciki har da ɗaurin rai-da-rai, saboda kama su da laifin yi wa Boko Haram canjin kuɗaɗe.
Sakamakon haka ne jami’an tsaro a Najeriya suka fara kamen wasu ‘yan canjin da ake zargi da tallafa wa ƙungiyar wajen yi musu safarar kuɗaɗe.
Mafi yawan mazajen da ake tsare da su fiye da shekara ɗaya ‘yan kasuwar canji ne da aka fi sani da wapa, kuma tun da aka kama su ba a bari iyalansu sun gan su ba in ban da kwanan nan, a cewar matan da suka shaidawa BBC.
Hukumomi na zargin mazajen nasu ne da taimaka wa ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta Boko Haram ta hanyar yi musu canjin kuɗin ƙasar waje.