fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Mataimakin shugaban kasa ya ce zai gaji kujerar Buhari a 2023

Date:

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Ya bayyana hakan ne a wani takaitaccen yada labarai da aka yada ta shafinsa na Twitter bayan shafe tsawon watanni ana ta cece-kuce.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Osinbajo, a liyafar cin abincin dare da ya shirya a fadar shugaban kasa a Villa, domin buda azumin watan Ramadan a ranar Lahadi, ya sanar da gwamnonin APC shirinsa na ya gaji maigidansa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), wanda wa’adin shugabancinsa zai kare nan da watanni 13.

Ya ce, “Na yi imanin cewa, dalilin da ya sa Allah Madaukakin Sarki Ya ba ni wadannan abubuwan da suka faru, da wadannan bayanai da kuma wadannan damammaki shi ne, dole ne a yi amfani da su wajen amfani da wannan kasa tamu mai girma da kuma al’ummarta masu girma.

“A dalilin haka ne a yau, cikin tawali’u, a hukumance na bayyana aniyara ta tsayawa takarar shugaban kasa a tarayyar Najeriya a karkashin babbar jam’iyyarmu ta All Progressives Congress.”

Osinbajo, wanda ya cika shekaru 65 a watan da ya gabata, babban mai ba da shawara ne ga Najeriya, kuma tsohon malami ne a jami’ar Legas. Shi ma babban Fasto ne a Cocin Redeemed Christian Church of God.

Ya fara aikin gwamnati ne a shekarar 1988 a matsayin mai ba da shawara (shawarwari da shari’a) ga babban mai shari’a kuma ministan shari’a, Bola Ajibola, mukamin da ya rike tsawon shekaru hudu.

breaking news in nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp