Mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan ya sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Olaniyan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Lahadi.
Ya ce shawarar ta zo ne domin biyan bukatar magoya bayansa da suka gaji da jira bayan sun ci gaba da zama a jam’iyyar PDP, na dan wani lokaci.
Ya ce sauya shekar bai shafi dangantakarsa da gwamnan jihar, Seyi Makinde ba, yana mai cewa ya ci gaba da tafiya tare da gwamnan kan harkokin mulki.
Ya ci gaba da cewa bai ajiye mukamin mataimakin gwamna ba.