Wasu masu zanga-zanga sun mamaye majalisar dokokin kasar nan da ke Abuja, saboda zaben shugaban kasa da aka kammala a kasar nan.
Masu zanga-zangar dai na dauke da kwalayen rubuce-rubuce irin su ‘Ceto Dimokuradiyyar mu’, “INEC + Cin Hanci da Rashawa, ‘Yan Siyasa suna kashe Dimokuradiyyarmu,” da “INEC na kashe Dimokuradiyyar Najeriya.”
Wannan dai na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan wata zanga-zangar da ta barke a dandalin Unity Fountain ranar Talata a Abuja.