fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Masu garkuwa sun saki malamin jami’ar Wudil

Date:

Masu garkuwa da mutanen sun sako malamin jami’ar da aka sace a jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano (KUST) Wudil, Huzaifa Karfi.

An saki Karfi ne da yammacin ranar Asabar. An yi garkuwa da shi ne a Zariya ranar Laraba a lokacin da ya je kai kudin fansa ga hakimin Karfi da ke karamar hukumar Takai a Kano, Abdulyahyah Ilu, wanda daga nan ya samu ‘yanci.

A baya dai an ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki tare da kashe mutane shida a kauyen Karfi da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano tare da yin garkuwa da basaraken mai shekaru 53 a duniya.

An ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne a kan babura uku daga jihar Bauchi ta dajin Ringim da ke Jigawa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, wakilinmu ya samu labarin cewa malamin da aka saki tare da wasu na kan hanyarsu ta komawa Kano.

punch newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp