fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Masu garkuwa sun kama mutane 23 ciki harda ‘ya’yan tsohon akanta na Zamfara

Date:

A kalla mutane 23 da suka hada da mata biyu da ’ya’yan tsohon akawun jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Bello, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su a garin Furfuri da ke karamar hukumar Bungudu a jihar.

Wani mazaunin yankin mai suna Malam Haruna Manaja Furfuri a wata hira da Blueprint ya ce ‘yan bindigar sun yiwa garin kawanya ne da misalin karfe 2:30 na safiyar ranar Litinin.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun je gidan tsohon akanta janar na Zamfara, inda suka yi garkuwa da matansa biyu, ‘ya’ya uku a yayin harin.

Malam Manaja ya kara da cewa matan biyu da aka yi garkuwa da su da sauran matan sun tsere bayan ‘yan sa’o’i da sace su.

“Bayan da jama’a suka bi sawun barayin cikin daji ne ‘yan fashin suka bar wadanda abin ya shafa suka gudu. Haka aka kubutar da wasu daga cikin wadanda aka sace da suka hada da mata biyu na Alhaji Abubakar Bello,” inji shi.

Ya ce har yanzu ‘ya’yan tsohon akantan janar din su uku har da wata budurwa da za a yi aure ba da jimawa ba suna cikin gidan ‘yan fashi.

“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, ‘yan fashin sun amsa ta wayar tarho suna neman kudi daga hannun akawun janar din a matsayin kudin fansa kafin su saki ‘ya’yansa uku,” inji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP. Muhammad Shehu, a wata hira da Blueprint ya tabbatar da faruwar lamarin.

jalingo news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp