Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun tare wata motar bas mai mutane 18, a kauyen Ochonyi- Omoko, daura da babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja a jihar Kogi.
Wani fasinja Benjamin Isaac da ya tsere ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:03 na daren Laraba.
Ya ce, maharan da suka boye a cikin daji sun bude wuta kan motar bas din, inda suka lalata tayoyin baya a cikin aikin.
“Sun bude wuta a kan tayoyin baya, lamarin da ya tilasta wa direban ya rasa yadda zai yi. A lokacin da direban motar ya kauce hanya, ‘yan bindigar sun fito daga inda suka buya suka umarci fasinjojin da su fito. Sun kai mu cikin daji da bindiga,” in ji shi, ya kuma kara da cewa ya yi nasarar tserewa tare da wasu fasinjojin da suka gudu cikin daji.
Isaac ya ce, ya hau motar bas ne a gefen titi a Zuba, a lokacin da yake tafiya zuwa Okpella, jihar Edo.
Wani dan banga da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yana alwala gabanin Sallar Isha’i ne, sai ya ji karar harbe-harbe.
“Bayan addu’a na ne na tuntubi abokan aikina kuma na zagaya wurin da lamarin ya faru, inda muka gano wata motar bas da ta yashe a gefen hanya ba tare da fasinjoji a ciki ba,” ya ce daga baya ya gano cewa an sace wasu fasinjojin da ke cikin motar.
Majiyar ‘yan banga ta ce, shi da abokan aikinsa na ci gaba da tseratar dajin domin zakulo ‘yan bindigar da kuma ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.
Rundunar ‘yan sandan jihar dai ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kogi, DSP Williams Ovye Ayah, har yanzu bai amsa kiran da aka yi masa da sakon da aka tura mas ba, kamar yadda The Will. ta rawaito.