Kafar yada labarai ta Al Jazeera ta bayyana cewa, hukumomi a Masar sun saki dan jaridar ta Ahmed El-Nagdy da suka tsare.
Wannan na zuwa ne yayin da shugaban kasar ta Masar Abdel Fattah al-Sisi ke ziyara a Qatar – wurin da kafar yada labaran ke yada shirye-shiryenta.
Haka-zalika, wannan ne kuma karon farko kenan tun bayan da kasashen biyu suka dawo da huldar dangantaka a shekara da ta wuce bayan rashin jituwa ta diflomasiyya.
An tsare El-Nagdy tsawon shekara biyu, inda har yanzu ake ci gaba da tsare abokanan aikinsa biyu.
Gwamnatin Masar karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Sisi ta sha kama ‘yan jaridan Al Jazeera kan abin da ta kira na yada labaran da basu dace ba da take yi