Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fitar da wata sanarwa, bayan hirar da dan wasanta Cristiano Ronaldo ya yi da fitaccen dan jarida dan kasar Burtaniya Piers Morgan.
Kwanan nan Ronaldo ya yi wata hira ta musamman da Morgan inda ya caccaki Manchester United da kocinta Erik ten Hag.
Kyaftin din Portugal ya ce Man United ta ci amanar sa kuma baya mutunta Ten Hag.
Sai dai yayin da take mayar da martani ga ci gaban, Man United, a cikin wata sanarwa ta shafinta na yanar gizo ranar Litinin, ta ce: “Manchester United ta lura da yadda kafafen yada labarai suka yada hirar da Cristiano Ronaldo ya yi.
“Kungiyar za ta yi la’akari da martanin ta bayan an tabbatar da cikakkun bayanai.
“Mayar da hankalinmu ya kasance kan shirya don rabin na biyu na kakar wasa tare da ci gaba da haÉ“aka, imani da haÉ—in kai tsakanin ‘yan wasa, manaja, ma’aikata, da magoya baya.”