Malaman Firamare da na Sakandare a fadin kasar Ghana sun ce, za su tsunduma yajin aiki saboda rashin biyan su kudaden su na alawus.
Malaman dai sun ce kudaden na alawus, wanda kashi 20 na albashinsu, yana da muhimmanci sosai domin zai rage musu wahala daga halin tabarbarewar tattalin arziki da kasar ke ciki.
Karuwar hauhawarar farashi da kasar ke fama da shi dai ba a taba ganin irin sa ba a cikin shekara 18, inda kasar mai albarkatun kasa da ke Afrika ta Yamma ke shirin ciyo bashi domin samun damar biyan ma’aikatan ta.
Ana sa ran wata tawaga daga asusun bada lamuni na duniya, IMF, za ta kai ziyara Ghana a makon nan domin fara tattaunawa da gwamnatin kasar domin taimaka mata.
Yajin aikin da malaman da ke koyarwa suka ayyana a yau Litinin ya shafi har da wadanda ba sa koyarwa.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Ghana ta gaza aiwatar da yarjejeniyar da ta cimma da shugabannin malaman suka ba ta ranar 30 ga watan Yuni. In ji BBC.