Majalisar dokokin jihar Zamfara ta amince da kudirin dokar hukunta duk wani laifi da ya shafi ‘yan fashi a jihar ta hanyar rataya.
SIYASAR NIGERIA ta gano cewa majalisar ta zartar da kudirin ne a ranar 28 ga watan Yunin 2022.
Ya ce, kudurin dokar ya tanadi hukunta masu ba da labari da duk wadanda ke da hannu wajen taimakawa da garkuwa da mutane, satar shanu, da kuma ‘yan fashi a jihar da ke fama da rikici.
A cewar ‘yan majalisar, masu ba da labari da ke ba da taimako ga ‘yan ta’adda za su fuskanci kisa ta hanyar rataya a bainar jama’a.
Da yake magana a kan kudurin dokar, Abdullahi Shinkafi, mashawarci na musamman kan harkokin gwamnati na gwamnan Zamfara, ya ce: “A yau, gwamna zai sanya hannu kan hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, masu ba da labari da duk wani lamari da ya shafi ‘yan fashi. ” in ji shi.
“Majalisar dokoki, jiya a Zamfara ta zartar da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, masu ba da labari da kuma masu bayar da gudummawa.”