Majalisar dokokin jihar Oyo ta tsige mataimakin gwamnan jihar, Injiniya Rauf Olaniyan, bayan da wani kwamiti mai wakilai bakwai da babban alkalin alkalan jihar ya kafa, domin binciken mataimakin gwamnan kan zargin aikata ba daidai ba ya bukaci hakan.
Rahoton kwamitin ya ce, an samu mataimakin gwamnan da laifi kan duka zarge-zargen da ake yi masa.
Duka ‘yan majalisar jam’iyyar PDP 23 da suka halarci zaman na yau sun aminci da bukatar kwamitin.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai babbar kotun jihar da ke ibadan ta yi watsi da karar da mataimakin gwamnan ya shigar gabanta yana neman kotun ta dakatar da ‘yan majalisar daga tsaige shi.
A kwanakin baya ne dai mataimakin gwamnan ya fice daga jam’iyya PDP mai mulkin jihar zuwa APC mai hamayya.