Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ta fara binciken lamuni da kuma tallafin da gwamnatin da ta shude ta Mallam Nasir El-Rufai ta karba daga kasashen waje da na cikin gida da ake ta cece-kuce a kai.
Majalisar ta kafa wani kwamiti da zai gudanar da binciken a zauren taron na ranar Talata wanda shugaban majalisar, Yusuf Liman Dahiru ya jagoranta.
An ba wa kwamitin alhakin fara binciken gaskiyar ma’amalar kudi da lamuni da tallafi da sauran ayyukan aiwatarwa tun daga 2015 har zuwa 2023.
Kwamitin binciken ya ba da umarnin gayyatar El-Rufai da wasu manyan mutane ciki har da tsohon shugaban majalisar wakilai ta 8 da ta 9.
Sauran wadanda za a gayyata sun hada da tsoffin kwamishinonin kudi da kuma tsoffin kwamishinonin kasafin kudi da tsare-tsare.
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya koka da dimbin bashin da gwamnatin da ta shude ta bari, wanda ya yi ikirarin gazawa gwamnatin sa.