fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Magoya bayan Adeleke na yin zanga-zanga a Osun

Date:

Biyo bayan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Osun ta yanke a ranar Juma’a, ga tsohon gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola, masu zanga-zangar sun tare manyan tituna a cikin babban birnin jihar Osogbo.

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa mazauna jihar da ke zanga-zangar sun tare hanyar Osogbo zuwa Ikirun, titin Gbongan-Ibadan, Oke-Fia, Old Garage da Freedom Park.

An dai ga yadda suka kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa, suna takurawa tare da dukan direbobin kananan motocin bas (korope).

Masu babura na kasuwanci su ma ba a bar su ba.

Ci gaban da aka samu ya sa matafiya da dama suka makale, kamar yadda yawancin ‘yan kasuwa da suka mallaki shaguna a kusa da gadar ba su bude harkokin kasuwanci ba.

Sai dai zanga-zangar ba ta bazu zuwa wuraren zama ba saboda harkokin yau da kullum na tafiya kamar yadda aka saba ba tare da tada hankali ba

Zanga-zangar ta kuma bazu zuwa garuruwa irin su Ikirun, Ilesa, Ilobu, Iwo, Ile-Ife da sauran garuruwan inda mazauna yankin suka fusata da hukuncin kotun, suma suka yi dandazo domin gudanar da zanga-zangar.

A halin da ake ciki kuma, jam’iyyar APC ta jihar Osun da ke nuna damuwarta ta bukaci babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Alkali Baba Usman da ya shiga tsakani tare da kawo karshen barazanar da ake yi wa rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar Osun.

vanguard (nigeria)

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...
X whatsapp