Mukaddashin gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya amince da murabus din da kwamishinan kula da albarkatun ruwa na jihar, Sadiq Aminu Wali, bisa radin kansa.
Kwamishinan wanda ya mika takardar murabus din ta ofishin mukaddashin gwamna a madadin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya shafe shekaru biyu yana aiki.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar, mukaddashin gwamnan ya yabawa kwamishinan mai barin gado, bisa hidimar da yiwa gwamnati da al’ummar jihar Kano.
Ya yi nuni da gamsuwa da nasarorin da aka samu a ma’aikatar, duk da kalubalen da ake fuskanta, a fannin samar da ruwan sha ga al’ummar da ke karuwa, musamman a babban birnin jihar.
Mukaddashin gwamnan ya yi matukar godiya ga kwamishinan da ke barin gado tare da yi masa fatan alheri. A cewar sanarwar da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar.