Kungiyoyin kwadago NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da suke yi a fadin kasar nan.
Wannan shi ne don ba da damar yin taro ba tare da katsewa ba tare da kwamitin bangarori uku kan sabon mafi karancin albashi na kasa.
Shugaban TUC, Festus Osifo ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata.
Shugabannin kungiyar kwadagon sun gana da sakataren gwamnatin tarayya, SGF, George Akume, da wasu jami’an gwamnati a ranar Litinin din da ta gabata inda suka cimma matsaya kan cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kuduri aniyar biyan mafi karancin albashi fiye da N60. ,00