fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Kungiyar Kwadago na taron gaggawa a kan yajin aiki

Date:

Kungiyar kwadago ta na cikin wani taron gaggawa na majalisar zartarwa ta kasa kan dakatar da yajin aikin da suka yi.

Wata majiya mai tushe a taron da ake ci gaba da yi a Abuja ta bayyana hakan ga manema labarai a safiyar ranar Alhamis.

A cewarsa, tuni shugabannin kungiyar ke tattaunawa kan yiwuwar dakatar da yajin aikin saboda ganawar da suka yi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba.

“Zai zama da wuri a ce mun dakatar da yajin aikin. Mun hadu ne don duba wannan zabin,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu.

A cewarsa, za a sanar da bayanan ganawar cikin sa’o’i.

DAILY POST ta tuna cewa NLC ta gudanar da zanga-zanga a fadin kasar domin neman a sauya tallafin man fetur da kuma karin albashin ma’aikata.

Sakamakon haka, shugabannin kungiyoyin kwadago sun gana da Tinubu a fadar Villa domin dakatar da kara yajin aikin.

Tinubu, a wata sanarwa da Dele Alake, mai magana da yawunsa ya fitar a daren Laraba, ya yi alkawarin biyan bukatun ma’aikata.

NLC ta sanar da fara yajin aikin a fadin kasar daga ranar 2 ga watan Agustan 2023.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...

Rikici ya kuma balle a Syria

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun ce, wani sabon rikici...

Tsofaffin ‘Yansanda na da ‘yancin yin zanga-zanga – A Cewar Amnesty

Ƙungiyar Amnesty International ta ce tsofaffin ƴansandan Najeriya girmamawa...

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...
X whatsapp