Babbar Kotun Jihar Legas da ke zamanta a Ikeja, ta yanke wa riƙaƙƙen wanda ake zargi da garkuwa da mutane Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans hukuncin ɗaurin rai da rai.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, an yanke wa Evans tare da muƙarrabansa Uche Amadi da Okwuchukwu Nwachukwu hukuncin ne bayan kotun ta same su da laifi kan wasu zarge-zarge biyu waɗanda suka haɗa da haɗa baki domin aikata laifi da kuma garkuwa da mutane.
Alƙali Hakeem Oshodi wanda ya yanke hukuncin, ya kama mutum ukun da laifin garkuwa da babban daraktan kamfanin haɗa magunguna na Maydon Pharmaceuticals Limited wato Donatus Dunu.
Ya bayyana cewa akwai cikakkun hujjoji da suka tabbatar da suna da laifi.