Mai shari’a Mobolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talata ya yanke wa Sufeto-Janar na ‘yan sanda Usman Baba hukuncin daurin watanni uku a gidan yari saboda ya ki bin umarnin kotu.
Mai shari’a Olajuwon wanda ya yanke hukuncin, ya ce, umarnin ya biyo bayan karar da wani tsohon jami’in ‘yan sanda, Patrick Okoli ya shigar inda ya ce, ya yi masa ritaya daga aikin ‘yan sandan Najeriya ba bisa ka’ida ba kuma tilas. A cewar Daily Post.