Kotun kolin masana’antu ta kasa, ta umarci kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), da ta janye yajin aikin da ta shiga.
PlatinumPost ta ruwaito cewa, aikin masana’antar ya dauki tsawon watanni bakwai.
Kotun ta yi amfani da sashe na 18 na dokar takaddamar ciniki da kuma bukatun kasa na daliban Najeriya da su amince da bukatar gwamnatin tarayya na neman umarnin hukunta malaman.
Mai shari’a Polycap Hamman ta bayar da umarnin dakatar da yajin aikin ne yayin da ta ke yanke hukunci a wata takardar da gwamnatin tarayya ta shigar na neman a tilasta wa malaman jami’o’in su koma bakin aiki har sai an warware musu bukatunsu na kyautata yanayin aiki.


