Kotun daukaka kara ta jihar Kano, a ranar Juma’a ta sake tabbatar da Sadiq Aminu Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Kano.
A wani hukunci na bai daya da ta yanke a ranar Juma’a, kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke na tabbatar da Muhammad Abacha a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na PDP.