Kotun koli ta tabbatar da Chukwuma Odii Ifeanyi a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Ebonyi a zaben 2023 mai zuwa.
Kotun ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a kan Sanata Joseph Obinna Ogba saboda rashin bin doka da oda.
A hukuncin da mai shari’a Mohammed Lawal Garba ya yanke kuma wasu alkalai hudu suka amince da shi, kotun kolin ta ce bai kamata kotun daukaka kara ta saurari Ogba ba saboda bai samu izinin kotu ba kafin ya shigar da kara a kotun daukaka kara.
Mai shari’a Garba ya daure tunda Sanata Ogba baya cikin karar babbar kotun tarayya, ya kamata ya nemi kotun daukaka kara kuma ya samu izinin shiga lamarin.