Wata babbar kotun tarayya dake Uyo ta soke zaben Akanimo Udofia a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Akwa Ibom.
Mai shari’a Agatha Okeke, wanda ya yanke hukuncin ya umarci jam’iyyar APC da ta gudanar da sabon zaben fidda gwani na gwamna cikin kwanaki 14.
Wani tsohon Sanata, Ita Enang ne ya shigar da karar, inda ya yi ikirarin cewa shi ne sahihin dan takarar jam’iyyar APC a Akwa Ibom.
Mai shari’a Okeke ya amince da hujjar Mista Enang, kuma ya yanke hukuncin cewa Udofia ba dan jam’iyyar APC ba ne saboda bai shiga dukkan matakai na zaben dan takarar gwamna na jam’iyyar ba.