Babbar kotun tarayya da ke Yola, ta soke tikitin jam’iyyar PDP na takarar kujerar Sanatan Adamawa ta tsakiya.
An ayyana kakakin majalisar dokokin jihar, Aminu Abbas ne a matsayin wanda ya lashe tikitin takara a lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan majalisar dattawa na jam’iyyar PDP a farkon shekarar.
Wata babbar kotun tarayya karkashin jagorancin mai shari’a Abdulaziz Anka, ta yanke hukuncin a ranar Litinin cewa shigar Awwal Tukur a matsayin dan takarar siyasa a zaben fidda gwani ya bata dukkan tsarin.
Daya daga cikin wadanda suka yi takarar tikitin takara da shugaban majalisar, Abubakar Ibrahim ne ya shigar da karar, inda ya ce baya ga batun Awwal Tukur na cewa wadanda ba wakilai ba ne suka kada kuri’a a zaben fidda gwani.
Kotun da ta yanke hukuncin na ranar Litinin, ta mai da hankali kan shigar Awwal Tukur, inda ta zargi PDP da rashin gudanar da zaben fidda gwanin da ya dace da dokokin da suka dace.
Kotun ta kammala da cewa jam’iyyar PDP ba ta da dan takara a zaben Sanatan Adamawa ta tsakiya da za a yi a badi.