Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, karkashin jagorancin mai shari’a M N Yunusa ta soke takarar zababben gwamnan jihar Abia, Dakta Alex Otti da daukacin ‘yan takarar jam’iyyar Labour a jihohin Abia da Kano.
Kotun ta ce fitowar su bai dace da tanadin dokar zaben 2022 ba.
Da safiyar Juma’a kotun ta yank hukuncin.
Kotun da ta shigar da kara mai lamba FHC/KN/CS/107/2023 da Mista Ibrahim Haruna Ibrahim ya shigar kan jam’iyyar Labour da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce jam’iyyar Labour ta gaza mika rajistar zama mambobinta ga INEC a cikin Kwanaki 30 kafin zabukan firamarensu ya sa tsarin ya zama mara inganci.
“Jam’iyyar da ba ta bi tanade-tanaden dokar zabe ba, ba za a ce tana da dan takara a zabe kuma ba za a iya bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zabe ba; saboda haka, kuri’un da aka baiwa wanda ake kara na 1, kuri’a ce ta bata,” inji alkalin.