Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abakaliki ta soke zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP da aka sake gudanarwa a jihar Ebonyi.
Kotun ta ce, zaben fidda gwanin da ya samar da Sanata Obinna Ogba da sauran ‘yan takara ya sabawa ka’ida, ba bisa ka’ida ba, ba shi da tushe balle makama.
Kotun ta kuma tabbatar da zaben fidda gwani da aka gudanar tun farko a jihar wanda ya samar da Dr Ifeanyi Odii a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP.