Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a garin Fatakwal na jihar Ribas ta soke dukkan zabukan fitar da gwani da jam’iyyar APC ta gudanar a jihar.
Ku tuna cewa wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka fusata masu biyayya ga Dan takarar Gwamna na SDP, Sanata Magnus Abe, sun tunkari Kotu suna kalubalantar yadda zaben fidda gwanin ya gudana tare da ikirarin cewa ba a yi zaben fidda gwani na wakilan da aka gudanar a jihar ba.