fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Kotu ta kori ‘yan takarar majalisa 14 na NNPP

Date:

Wata babbar kotun tarayya da ke Fatakwal a ranar Alhamis ta kori ‘yan takarar majalisar dokoki 14 na jam’iyyar New Nigeria People’s Party a jihar Ribas saboda rashin bin dokar zabe da jam’iyyar ta yi wajen gudanar da zabukan fitar da gwaninta.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar ta maka ‘yan takarar jam’iyyar NNPP a gaban babbar kotun tarayya tana neman a soke su.

Alkalin kotun, Mai shari’a Turaki Muhammed, a hukuncin da ya yanke, ya ce jam’iyyar PDP ta iya tabbatar wa kotu cewa jam’iyyar NNPP ba ta bin ka’idojin da aka gindaya a sabuwar dokar zabe a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyarsu.

Don haka alkalin ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta da ta daina amincewa da wadanda abin ya shafa a matsayin ‘yan takara.

Hukuncin na zuwa ne kwanaki kadan bayan wata babbar kotun tarayya da ke Fatakwal ta soke dukkan zabukan fidda gwani da jam’iyyar All Progressives Congress ta gudanar a jihar Ribas.

natforce latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...
X whatsapp