fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Kotu ta kori dan majalisar wakilai mai ci kuma dan takara

Date:

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja a ranar Litinin, ta kori dan majalisar wakilai mai ci, Hon Sani Umar Dan Galadima a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji na jihar Zamfara a zaben 2023 mai zuwa.

An fitar da dan majalisar ne daga takarar majalisar wakilai ta 2023 saboda kasancewarsa dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a lokacin da ya tsaya takarar fidda gwani a PDP.

Mai shari’a Inyang Edem Ekwo ya soke nasarar da dan majalisar ya samu a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP yayin da yake yanke hukunci a karar da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP biyu, Muzammil Mohammed Idris da Ibrahim Sani suka shigar a kansa.

Mai shari’a Ekwo ya bayyana cewa dan majalisar, tun da bai yi murabus ba, ko ya sauya sheka ko kuma ya tsallake rijiya da baya daga APC zuwa PDP a cikin lokacin da doka ta kayyade, ba halalcin dan PDP ba ne, kuma ba zai iya tsayawa takara a kowane zabe a dandalinta ba.

Mai shari’a Ekwo ya yi amfani da sashe na 221 na kundin tsarin mulkin 1999, sashe na 84 na dokar zabe ta 2022 da sashe na 50 (4) na jam’iyyar PDP da su soke zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da ya samar da shi.

Wadanda ake tuhumar sun hada da Hon Sani Umar Dan Galadima, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, Jam’iyyar PDP da Dr Iyorchia Ayu.

Mai shari’a Ekwo ya bayyana cewa tun daga kan doka ya kamata dan majalisar ya fice daga jam’iyyarsa ta APC kwanaki 30 gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP kafin ya samu damar zama dan takarar PDP.

Kasancewar ya ci gaba da zama a APC a lokacin da ya sayi fom din nuna sha’awa da kuma fom din tsayawa takara a PDP, ya yi kuma ya mika fom din, babu yadda za a yi ya zama dan takarar jam’iyyar.

Daga nan ne alkalin ya bayar da umarnin haramtawa tare da hana dan majalisar bayyana kansa a matsayin dan takarar PDP.

Mai shari’a Ekwo ya sake bayar da wani umarni ga jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da sabon zaben fidda gwani da nufin zaben sabon dan takarar mazabar tarayya ta Kaura Namoda/Birnin Magaji a zaben 2023.

legit new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ĉ´ansandan jihar Kaduna, sun buĈ™aci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi Ĉ™ungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban Ĉ™aramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp