Wata babbar kotun jihar Oyo da ke zamanta a Ibadan, ta hana majalisar dokokin jihar ci gaba da batun tsige mataimakin gwamnan jihar Injiniya Rauf Aderemi Olaniyan.
Kotun karkashin jagorancin mai shari’a, Ladiran Akintola, ta bayar da wannan umarni a ranar Laraba.
DAILY POST ta tuna cewa, a kwanakin baya Majalisar ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan.
Majalisar ta yi zargin cewa, mataimakin gwamnan ya aikata wasu laifuka.
Hakan ya sa mataimakin gwamnan ya garzaya kotu domin dakatar da tsige shi.
A ranar Laraba ne dai kotun ta hana ‘yan majalisar cigaba da tsige mataimakin gwamnan.
Akintola ya yanke hukuncin cewa majalisar dokokin jihar ta dakatar da duk wani tsari na tsige shi.
Alkalin, a cikin jawabinsa, ya dage sauraron karar zuwa ranar Talata, 5 ga Yuli, 2022.