Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a yau Talata ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin zaman gidan yari na shekara shida.
Mutanen wato Chibunna Patrick Umeibe da kuma Emeka Alphonsus Ezenwane waÉ—anda ake yi wa shari’a tare da DCP Abba Kyari, an kama su ne da laifuka uku daga cikin laifukan da hukumar NDLEA da ke yaÆ™i da safarar miyagun Æ™wayoyi ta shigar game da su.
An kama mutanen biyu ne a filin jirgin sama na Enugu a yayin da suke ƙoƙarin fasa ƙwabrin hodar ibilis.