fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Kotu ta dage shari’ar tsofaffin kudi da sababbi

Date:

Kotun Ƙolin Najeriya ta ɗage zaman sauraren shari’ar da wasu gwamnonin jihohin ƙasar suka shigar kan ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar na takardar naira 200 da 500 da 1,000.

Kotun ta ɗage zaman ne bayan da wasu jihohi guda tara suka bi sahun gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara waɗanda suka shigar da ƙarar tun da farko.

Jihohin da ke ɓangaren masu ƙarar bayan guda ukun na farko su ne Kano da Katsina da Sokoto da Lagos da Ondo da Ogun da Ekiti da Rivers.

Ita ma a ɓangarenta gwamnatin ƙasa ta samu jihohin Edo da Bayelsa a matsayin waɗanda ke kare ta a shari’ar.

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai da takwaransa na jihar Kogi Yahaya Bello sun halarci Kotun a yau.

Yanzu dai al’umma za su ci gaba da jira har zuwa 22 ga watan Na Fabrairu kafin sanin matsaya game da ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin ko kuma a’a.

Gwamnatocin jihohin Kaduna, da Zamfa da kuma Kogi ne suka shigar da ƙarar, inda tun farko kotun ta bayar da umurnin jingine wa’adin daina amfani da takardun kuɗin na 10 ga watan Fabrairu, wanda bankin ya bayar a farko.

Mutane dai a Najeriya sun shiga ruɗani a kan ko za su iya ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin na naira 1,000, da 500, da 200 duk da umurnin da kotu ta bayar na jingine wa’adin na 10 ga watan Fabrairu.

Haka nan rahotanni daga wurare da dama sun nuna cewa bankuna sun daina karɓar tsofaffin takardun kuɗin, suna bayar da hujjar cewa umurni ne suka samu daga Babban Bankin na Najeriya.

Bugu da ƙari wasu masu ƙananan sana’o’in da dama sun daina amsar tsofaffin kuɗaɗen.

taraba state today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp