An dage shari’ar dan fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu, har zuwa ranar 8 ga watan Afrilun 2022 domin yanke masa hukunci.
Rahotanni sun bayyana cewa, a ranar Larabar nan ne aka ci gaba da shari’ar jagoran ‘yan awaren. Ana tuhumar Kanu da laifuka 15 da suka hada da ta’addanci, cin amanar kasa, tada zaune tsaye da kuma gudanar da haramtacciyar kungiyar.
Kanu wanda ke shugabantar haramtacciyar kungiyar ‘yan awaren Biafra (IPOB), a baya ya musanta zargin da ake masa.
Lauyan Kanu, Mike Ozekhome, ya yi jayayya cewa, laifuffukan da ake zargin Kanu ya aikata ba su da tushe, inda ya ce, ba a bayyana inda suka aikata da kuma lokacin da suka aikata ba. Ya kuma bayyana cewa Najeriya ba ta da hurumin yanki.
A yau ne ake gudanar da zanga-zangar neman a sake shi a sassan Turai, ciki har da Jamus, a gaban gine-ginen Majalisar Dinkin Duniya (UN) a birnin Bonn.