Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta dage zamanta zuwa ranar Laraba 10 ga watan Mayu, batutuwan da suka gabatar gabanta na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023.
Daya daga cikin mai magana da yawun jamâiyyar Labour Party, LP, Kenneth Okonkwo, ne ya bayyana hakan a wani sakon Twitter a ranar Litinin.
Okonkwo ya rubuta: “Bayan takaitaccen shari’ar kafin sauraren karar, an dage sauraron karar zuwa ranar Laraba, 10 ga Mayu, 2023 da karfe 2 na rana.”
Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta fara aiki a Abuja, ranar Litinin.
Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, da takwaransa na jam’iyyar Labour, LP, Peter Obi suna kalubalantar ayyana Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.